Isa ga babban shafi

Akalla mutane 32 suka mutu a sabon rikici da ya kuno kai a Libya

Ma’aikatar lafiya a Libya ta bayyana cewa rikicin da ya barke tsakanin masu mara wa gwamnatocin kasar biyu da ke hamayya da juna, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 32, sannan wasu kusan 160 suka samu raunuka, tare da haifar da fargabar barkewar wani sabon rikici

Rikicin kasar Libya
Rikicin kasar Libya REUTERS - STRINGER
Talla

Kungiyoyin da ke dauke da makamai sun yi musayar wuta da ta lalata asibitoci da dama tare da cinnawa gine-gine wuta tun daga yammacin ranar Juma'a, fadan da ya yi mummunan tasiri a babban birnin kasar ta Libya tun bayan da aka tsagaita bude wuta a shekara ta 2020.

Fadan dai ya biyo bayan takun saka tsakanin magoya bayan Abdulhamid Dbeibah da Fathi Bashagha, wadanda matsayin firaministoci da ke jagorantar gwamnatocin da ke gaba da juna, sannan kowanne ke fafutukar ganin ya mallaki kasar da ke arewacin Afirka, wadda ke fama da tashe-tashen hankula tun shekara ta 2011.

Gwamnatin Dbeibah ta kafu ne a babban birnin kasar a matsayin wani bangare na shirin zaman lafiya da Majalisar Dinkin Duniya ke jagoranta bayan kawo karshen yakin a shekarar 2020, inda yake cewa kamata ya yi gwamnati mai zuwa ta kasance ta samu ne a sanadiyyar zabe.

Majalisar dokokin Libya mai mazauni a gabashin kasar ce ta nada Bashagha a farkon wannan shekarar, kuma tana samun goyon bayan babban hafsan soji na gabacin Khalifa Haftar, wanda yunkurinsa na kwace babban birnin kasar da karfi a shekarar 2019 ya koma yakin basasa na tsawon shekara guda.

Kasar Libya dai ta fada cikin rudani ne tun bayan hambarar da gwamnatin shugaba Mo’amer Kadhafi a shekara ta 2011 tare da kashe shi a wani boren da kasashen yamma ke marawa baya, inda aka samu  kungiyoyi masu dauke da makamai da kuma wasu kasashen ketare suka yi yunkurin cike gurbin madafun iko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.