Isa ga babban shafi

Jami'an tsaron gabar tekun Libya sun tsamo gawar 'yan ci-ranin Mali 22 a ruwa

Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da mutuwar ‘yan cirani 22 ciki har da kananan yara 3 da suka fito daga Mali a kokarinsu na tsallakawa Turai ta gabar tekun Libya, bayan ceto wasu abokanan tafiyarsu 61 a tsakar tekun Mediterreniya.

Libya ta kasance babbar hanyar da 'yan cirani ke amfani da ita don shiga turai.
Libya ta kasance babbar hanyar da 'yan cirani ke amfani da ita don shiga turai. AP - Pau de la Calle
Talla

Hukumar kula da kaurar baki ta Majalisar Dinkin Duniya da ke tabbatar da batun kifewar kwale-kwalen ‘yan ciranin a takar teku, ta ce wadanda suka tsira daga ibtila’in sun labarta mata irin wahalar da suka sha da kuma yadda abokanan tafiyarsu 22 suka nutse ciki har da kananan yara 3.

Kakakin hukumar Safa Msehli ta ce ‘yan ciranin sun shafe kwanaki 9 a tsakiyar teku gabanin samun daukin jami’an kula da gabar teku na Libya da suka yi nasarar kaisu gabar ruwa.

Safa Msehli ta ce jirgin kwale-kwalen ‘yan ciranin wanda na roba ne ya tashi daga gabar ruwan birnin Zuwara na Libya da ke gab da iyakar Tunisia da misalin karfe 1 na daren ranar 22 ga watan Yunin da ya gabata inda suka shafe kwanaki 9 akan ruwa gabanin jami’an su isa garesu.

A cewar jami’ar galibin ‘yan ciranin 22 da suka mutu a tafiyar sun nutse ne a teku yayinda kishirwa ta yi ajalin wasu yayinda aka yi nasarar ceto wasu 61.

Hukumar ta IOM ta ce da yawa daga cikin ‘yan ciranin yanzu haka na cikin mawuyacin hali inda su ke karbar kulawa a asibiti yayinda wasu da suke cikin koshin lafiya aka tisa keyarsu zuwa sansanin killace bakin haure na Al Maya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.