Isa ga babban shafi

MDD ta gano manyan kaburbura dauke da tarin gawarwaki a Libya

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci hadin kan mahukuntan Libya don zurfafa bincike bayan gano wasu tarin kaburbura da aka birne mutane fiye da 100 a wani kauye da ke yammacin birnin Tripoli.

Wani yanki da aka gano manyan kaburbura a yankin Tahouna na yammacin Libya.
Wani yanki da aka gano manyan kaburbura a yankin Tahouna na yammacin Libya. REUTERS - ISMAIL ZITOUNY
Talla

Tawagar Majalisar Dinkin Duniya da ke bincike kan take hakkin dan adam a kasar ta Libya ta sha alwashin ci gaba da bincike bayan gano kaburburan dauke da gawarwakin mutane fiye da dari kowannensu wadanda ke a yankin Tarhouna na yammacin kasar.

Gano kaburburan na tawagar Majalisar Dinkin Duniyar na zuwa ne bayan mahukuntan Libya sun sanar da gano wani babban kabari na daban dauke da gawarwaki 247 duk dai a yankin na Tahouna, inda jami’an da suka yi aikin bude kabarin suka ce har a lokacin da dama daga cikin gawarwakin na sanye da ankwa a hannayensu.

Cikin makon nan ne tawagar ke shirin gabatar da rahoto na musamman mai shafuka 51 game da take hakkin dan adam din da kungiyar Kaniyat mai rike da makami ta yi a kasar ta Libya daga shekarar 2016 zuwa 2020.

Cikin rahoton tawagar Majalisar har da bayanin wasu mutane 7 iyalan gida guda da ke garkuwa da safara baya ga azabtarwa harma da kashe tarin fararen hular da ba su ji ba basu gani ba, ta yadda su ke kulle mutane a wani kankanin daki da suka kira da kurkuku.

Galibin wadanda tawagar ta samu a kurkukun sun kunshi mata da kananan yara da kuma tsofaffi sai kuma nakasassu da baza su iya tserewa daga hannun 'yan garkuwar ba.

Tawagar ta ce kungiyar ta Kaniyat da iyalan gida guda ke tafiyarwa, na samun umarnin daga wasu kwamandoji 4 da ba a kai ga gano su ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.