Isa ga babban shafi

Masu zanga-zanga sun afkawa majalisar dokokin Libya

Kafofin yada labaran kasar Libya sun rawaito cewa, masu zanga-zanga sun kutsa kai cikin ginin majalisar dokokin kasar da ke birnin Tobruk a gabashin kasar domin bayyana bacin ransu kan tabarbarewar yanayin rayuwa da kuma rashin alkibilar siyasar kasar.

Wasu daga cikin daruruwan masu zanga-zanga kan matsin rayuwa a birnin Tripoli a kasar Libya. 1 ga Yuli, 2022.
Wasu daga cikin daruruwan masu zanga-zanga kan matsin rayuwa a birnin Tripoli a kasar Libya. 1 ga Yuli, 2022. © REUTERS/Hazem Ahmed
Talla

Kafofin yada labarai da dama sun ruwaito cewar, masu zanga-zangar sun yi nasarar kutsawa cikin ginin majalisar dokokin kasar ta Libya tare da yin barna, yayin da daga kewayensa fusatattun matasa suka rika kona tayoyi.

Wasu rahotannin ma sun ce an kone wani bangare na zauren majalisar, wanda babu kowa a cikinsa, la’akari da cewar ranakun Juma’a a matsayin karshen mako a Libya.

Majalisar dokokin Libya, ta kasance a birnin Tobruk, mai tazarar daruruwan kilomita daga Tripoli babban birnin kasar, tun bayan rabewar kasar zuwa tsagin gabas da yamma a shekara ta 2014, sakamakon kazamin rikicin da ya biyo bayan boren da ya kifar da gwamnatin tsohon shugaba marigayi Moamer Ghaddhafi a shekara ta 2011.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.