Isa ga babban shafi

Kishirwa ta kashe 'yan ci-rani 20 a kokarinsu na shiga Libya

Masu aikin ceto a kan iyakar Chadi da Libya sun sanar da gano gawarwakin ‘yan cirani 20 a cikin hamada, wadanda alamu ke nuna tsananin kishirwa ne ya yi sanadin mutuwarsu.

Wasu 'yan cirani a Libya.
Wasu 'yan cirani a Libya. AFP - FATHI NASRI
Talla

Tawagar masu aikin ceton ta sanar da gano gawarwakin ne a kudu maso gabashin yankin Kufra mai nisan kilometre 120 daga Libya.

Sanarwar masu aikin ceton ta ce alamu na nuna motar 'yan ciranin ce ta samu matsala a tsakar sahara lokacin da su ke kokarin shiga Libya daga Chadi ko dai don shiga Turai ko kuma don gudanar da kasuwanci a Libyan wadda ta yi fama da yakin basasa tsawon shekaru 10.

Hotunan gawarwakin 'yan ciranin sun rika yawo a shafukan sada zumunta tare da motar da ke dauke dasu a tsakar saharar.

Dubban 'yan cirani ke mutuwa kowacce shekara a sahara, galibi saboda yunwa ko kishiryawa, baya ga wasu da rairayi kan birnewa.

Libya na matsayin babbar hanyar da 'yan cirani kan yi amfani da ita don shiga Turai ta tekun meditereniya sai dai da yawa daga ciki kan gamu da ajalinsu ba tare da nasarar kai wa inda suka nufa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.