Isa ga babban shafi

Libya: An gano gawarwaki bakwai a cikin wani sabon kabari

An gano gawarwaki bakwai da ba a kai ga tantancewa ba a Tarhouna, wani gari da ke yammacin Libya inda aka gano dimbin kaburbura tun daga shekarar 2020, kamar yadda hukumar binciken wadanda suka bata ta kasar ta fitar da sanarwa.

Kaburburan da aka gano a Tarhuna kenan, da ke kudu maso gabashin Tripoli babban birnin kasar Libya
Kaburburan da aka gano a Tarhuna kenan, da ke kudu maso gabashin Tripoli babban birnin kasar Libya AFP
Talla

Sanarwar da hukumar ta fitar ta ce, a ranar Lahadin da ta gabata ne aka gano wani “sabon kabari” a wani fili, inda aka tono gawarwaki bakwai.

Tarhouna dai wani karamin gari ne na manoma inda aka samu gawarwaki sama da 250 a cikin kaburbura tun lokacin bazara a shekarar 2020.

An ba da rahoton kasancewarsu a karon farko bayan ficewar sojojin Marshal Khalifa Haftar, mai karfin iko a gabashin Libya, daga yankin a shekarar 2020.

Tun a watan Afrilun 2019 ne wadannan dakarun suke kokarin mamaye Tripoli babban birnin kasar mai tazarar kilomita 80 daga arewa maso yamma, kuma inda tsohuwar gwamnatin da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ita ke da karfin iko.

A shekarar 2015 ne aka fara kai hare-hare a garin Tarhouna, lokacin da mayakan Al-Kani na yankin da aka fi sani da Kaniyat suka mamaye garin.

Mutum shida ne suka jagoranci kungiyar, inda ta rika yakar mazauna garin da sunan kawar da abokan hamayya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.