Isa ga babban shafi

Amurka ta umarci biyan diyyar wadanda harin cocin Lutheran ya shafa a Liberia

Wata kotu a jihar Pennsylvania ta Amurka ta yi umurnin biyan diyyar kudaden da jumullarsu ta kai dala miliyan 84 ga wasu mutane 4 da harin da aka kai wani cocin Lutheran ya shafa, daya daga ciki hare-hare mafi muni a lokacin yakin basasa da aka yi a Liberia a tsakanin shekarar 1989 zuwa 2003, inda sama mutane 600 suka mutu.

Peterson Sony, guda cikin wadanda suka tsira daga harin na majami'ar St. Peter's Lutheran a Liberia lokacin yakin basasar kasar.
Peterson Sony, guda cikin wadanda suka tsira daga harin na majami'ar St. Peter's Lutheran a Liberia lokacin yakin basasar kasar. © RFI/Darlington Porkpa
Talla

Hukuncin na zuwa ne bayan da kotu ta dora alhakin kashe-kashen a kan daya daga cikin kwamandojin sojin Samuel Doe, wanda kafin yanzu ya ke zaune a Pennsylvania, amma yanzu aka ce ya koma Liberia ya na rayuwa cikin walwala.

A wancan lokacin, mayakan ‘yan tawaye a karkashin jagorancin Charles Taylor ne ke yaki da dakarun gwamnatin Liberia a wajen babban birnin kasar, Monrovia, an kuma zargi sojojin gwamnatin Samuel Doe da aikata kisan.

Cibiyar shari’a da tabbatar da adalci ta San Francisco da ke Amurka ce ta wakilci wadanda wannan lamari ya rutsa da su.

Sai dai babu karin bayani a kan yadda kotun Amurkar ke shirin rinjayar mahukuntan Liberia su ba ta hadin kai wajen tabbatar da biyan wannan diyya ga wadanda abin ya shafa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.