Isa ga babban shafi
Liberia

An yanke hukuncin daurin shekaru 20 kan tsohon madugun 'yan tawayen Liberia

Kotu a Switzerland ta yanke hukuncin daurin shekaru 20 kan wani tsohon kwamandan mayakan ‘yan tawaye a Liberia, bayan samunsa da laifukan aikata Fyade, kisan gilla, da cin naman mutane.

Harabar babbar kotu a Switzerland da ta yanke hukuncin daurin shekaru 20 kan tsohon madugun 'yan tawayen kasar Liberia Alieu Kossiah.
Harabar babbar kotu a Switzerland da ta yanke hukuncin daurin shekaru 20 kan tsohon madugun 'yan tawayen kasar Liberia Alieu Kossiah. © Emma Farge / Reuters
Talla

Karo na farko kenan da wata kotun farar hula ke yanke irin wannan hukuncin kan tsohon madugun ‘yan tawayen kungiyar ULIMO mai suna Alieu Kossiah da ya jagoranci tayar da kayar baya ga dakarun tsohon shugaban Liberia Charles Taylor a shekarun 1990.

Kosiah da ya fuskanci tuhume-tuhume har 25 ciki har da cin zuciyar dan adam, ya shiga hannun jami’an tsaro a kasar Switzerland ne a shekarar 2014, kasar da yake zaune bayan samun takardar izinin zama ta dindindin.

A karkashin dokokin Switzerland da aka yiwa kwaskwarima a 2011, kotunan kasar na da hurumin hukunta manyan laifukan da aka aikata ko da kuwa ba cikin kasar ba ne ko nahiyar da take.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.