Isa ga babban shafi

MDD na fargabar ayyana yunwa a matsayin annoba a gabashin Afirka

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mummunan fari mai cike da tarihi a Somaliya ya raba mutane miliyan daya da muhallansu tare da barin kasar cikin tsananin yunwa.

Wata mata zaune da yaronta a wani asibiti yayin da yake karbar magani saboda rashin abinci mai gina jiki a garin Dadaab da ke kan iyaka da kasar Kenya.
Wata mata zaune da yaronta a wani asibiti yayin da yake karbar magani saboda rashin abinci mai gina jiki a garin Dadaab da ke kan iyaka da kasar Kenya. ASSOCIATED PRESS - Schalk van Zuydam
Talla

Sama da mutane 755,000 ne suka tsere daga gidajensu amma suna cikin iyakokin kasar, wanda idan aka hada da wadanda suka yi gudun hijira a kasashen waje, adadin ya kai miliyan guda, in ji hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya.

Somaliya da makwabtanta a yankin kuryar gabashin Afirka da suka hada da Habasha da Kenya na fuskantar fari mafi muni da ba a taba samu ba a cikin shekaru sama da 40 bayan da aka rasa ruwan sama har tsawon shekaru hudu a jere, abin da ya sanya rashin noma da kuma kashe dabbobi.

Binciken masana ya nuna cewa akwai yuwuwar rashin samun ruwan sama a shekara ta biyar, abin da ake fargabar zai raba iyalai da yawa.

Mohamed Abdi, darektan hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Norway a Somaliya ya ce "Wannan kalubale dake raba miliyoyin mutane da iyalansu, ya kasance babbar baraza ga kasar Somaliya."

Yace yanzu haka yunwa ta addabi kasar baki daya. Ana kuma ganin yadda iyalai da yawa ke barin komai saboda a zahiri babu ruwa ko abinci da ya rage a kauyukansu. Akwai bukatar a inganta hanyoyin samar da kudaden agaji kafin lokaci ya kure.

Ana sa ran adadin mutanen da ke fuskantar matsalar yunwa a Somaliya zai karu daga kimanin miliyan biyar zuwa sama da miliyan bakwai nan da watanni masu zuwa, sakamakon sauyin yanayi da hauhawar farashin abinci da yakin Ukraine ya haddasa, in ji MDD.

MDD ta koka bisa halin da ake ciki a yankin

Hukumar Abinci da Aikin Noma ta Majalisar Dinkin Duniya (FAO) ta yi gargadin cewa za a iya fuskantar babban hadarin yunwa a yankuna takwas nan da watan Satumba, idan aka kara samun karancin amfanin gona da kiwo, farashin kayayyaki zai ci gaba da hauhawa, sannan kuma taimakon jin kai zai fuskanci kalubale mai tarin yawa.

MDD ta ce duniya ba za ta iya jira a bayyana yunwa a matsayin annoba a hukumance ba a kuryar gabashin Afirka, inda za a fara fadin tashin yadda za a dauki matakin ceton rayukan al'umma, don haka akwai bukatar gwamnatoci su dauki matakan gaggawa kafin lokaci ya kure.

Wannan na zuwa ne yayin da hukumomin bada agaji na duniya ke ci gaba da cewa akwai karancin kudade a bangaren bada agaji, yayin da matalautan kasashe ke fama da kalubalen yunwa.

Somalia ta jima tana fama da matsalar mayakan jihadi

Tun a shekara ta 1991 ne dai Turawan mulkin mallaka na Birtaniyya suka ayyana ‘yancin kai ga Somaliya amma matakin bai samu amincewar kasashen duniya ba, lamarin da ya bar yankin na kuryar gabashin Afirka da ke da kusan mutane miliyan hudu cikin talauci da zama saniyar ware.

Sai dai ‘yan kasar sun kasance cikin kwanciyar hankali duk da cewa Somaliya na fama da yakin basasa, shekaru da dama da suka gabata, yayin da tashe-tashen hankula na siyasa da kuma tawaye na masu ikirarin jihadi da ke ci gaba da yiwa kasar barazana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.