Isa ga babban shafi

AU ta bayyana damuwa da rikicin kan iyaka tsakanin Sudan da Habasha

Kungiyar tarayyar Afrika ta bayyana damuwa da rikicin da ke tsakanin kasashen Sudan da Habasha inda ta yi kira da tattaunawa tsakanin kasashen biyu makwabtan juna don dinke barakar da ke tsakaninsu.

Firaministan Sudan Abdalla Hamdok tare da takwaransa na Habasha Abiy Ahmed yayin wata tattaunawarsu a birnin Khartoum.
Firaministan Sudan Abdalla Hamdok tare da takwaransa na Habasha Abiy Ahmed yayin wata tattaunawarsu a birnin Khartoum. © AFP Photo / Handout / Sudan Foreign Media Council
Talla

Cikin wata sanarwa da AU ta fitar ta ruwaito shugaban Majalisar kungiyar Moussa Faki Mahamat na cewa abin damuwa ne matuka yadda rikicin kasashen biyu makwabtan juna ke ci gaba da tsananta.

Kalaman Faki, na zuwa bayan Sudan ta zargi Sojin Habasha da keta kan iyaka tare da kisan dakarunta biyu a yankin da su ke takaddama akanshi da ke iyakokin kasashen biyu, batun da tuni Addis Abba ta musanta.

Shugaban na Majalisar AU, ya mika sakon jajantawa ga Sudan kan kisan dakarun na ta 7 yayinda ya roki sasantawa ta hanyar shiga tattaunawa tsakanin bangarorin biyu da Faki ya bayyana da ‘yan uwan juna.

A litinin din da ta gabata ne Sudan ta janye jakadanta da ke Addis Ababa tare da shan alwashin shigar da korafi gaban kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya don tuhumar Habasha da laifin keta tsaron iyaka.

Sai dai Habasha ta ci gaba da musanta zargin na Sudan wanda ta ce tun farko Sojin Khartoum suka fara tsallako mata iyaka, wanda ya kai ga musayar wuta tsakaninsu da mayaka masu rike da makamai a yankin, kuma lokacin da lamarin ya faru babu Sojinta ko guda a yankin.

Jaridar Tribune a Sudan ta ruwaito cewa Sojin kasar sun kaddamar da farmaki kan dakarun Habasha a yankin Al-Fashaqa jiya talata, said ai ma’aikatar tsaron kasar ta musanta batun.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.