Isa ga babban shafi

Hukumar shari'a a Tunisiya ta yi watsi da korar alkalai da shugaban kasar ya yi

Hukumomin shari'a a Tunisia sun soke korar da shugaban kasar Kais Saied yayi ya yiwa alkalai kusan 50 a farkon watan Yuni.

Shugaba Kais Saied, na kasar tunisia
Shugaba Kais Saied, na kasar tunisia AFP - FETHI BELAID
Talla

Matakin shugaban kasa na ranar 1 ga watan Yuni na sallamar alkalai 57 a kasar da ke arewacin Afirka,na zuwa ne bayan ya zargi da dama da cin hanci da rashawa da sauran laifuka.

Matakin nasa, wanda kungiyoyin kare hakkin bil-Adama suka kira "babban rauni ga 'yancin shari'a", ya haifar da yajin aikin alkalai a fadin kasar.

Hamsin da uku daga cikin wadanda aka kora ciki har da wasu da ake zargi da neman matan da ba muharramansu ba wadanda suka shigar da kara gaban kotun gudanarwa kan yunkurin Saied.

Kakakin ma'aikatar shari'a na kasar, Imed Ghabri ya ce an soke korar alkalai 46 da matakin ya shafa, ya kara da cewa an yi watsi da karar da wasu 7 suka shigar.

Kamar yadda bayanai daga kasar ke cewa, biyu daga cikin alkalan kuma suna jiran yanke hukunci, yayin da wasu biyu kuma ba su daukaka kara ba.

Lauyan Kamel Ben Messoud ya ce wadanda abin ya shafa za su iya ci gaba da aikinsu da zarar an samu takardar shaidar hukuncin da bangaren na shari'a suka yanke.

Dokar dai ta bawa shugaban kasar bai wa kansa ikon korar alkalai, kuma ya kori alkalai 57 bisa ka'ida, wanda ya kara tabbatar da kwace ikon da aka yi a watan Yulin bara lokacin da ya rushe majalisar dokokin kasar domin karawa kansa karfin iko, abin daq ya bashi damar dakatar da zaben majalisar dokoki.

Gamayyar kungiyoyin kare hakkin bil adama 10 a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar a lokacin, ta kira wannan mataki da aka yi a matsayin "kai hari ga bangaren doka".

A watan da ya gabata, Tunisiya  ta amince da sabon kundin tsarin mulkin da ya ba wa ofishin Saied karfin iko bayan wata kuri'ar raba gardama da bai yi kyau ba inda masu jefa kuri'a suka goyi bayan kundin.

Kuri'ar dai ta zo ne shekara guda bayan da Saied ya rushe gwamnati tare da dakatar da majalisar dokokin kasar a wani mataki mai ban mamaki ga dimokuradiyya, kuma daya tilo da ta fito daga boren kasashen Larabawa a shekara ta 2011.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.