IMF za ta ba Jamhuriyar Benin rancen sama da dala miliyan 600
Majalisar zartaswar asusun bada lamuni na duniya IMF ta sanar da cewa ta amince ta bai wa kasar Jamhuriyar Benin rancen dala miliyan 638 don tsamo kanta daga matsalar tattalin arziki da yakin da ake yi a Ukraine da kuma annobar covid 19 suka janyo mata.
Wallafawa ranar:
A wata sanarwa, asusun bada lamunin na duniya ya ce biyo bayan wannan shawarar ta majalisar zartaswarsa, za a aike wa da Benin din dala miliyan 143 ba tare da bata lokaci ba.
Asusun ya yaba da ci gaban da Benin ta samu a fannin kanana da matsakaitan masana’antu, wanda ya ce shine ginshikin tattalin arzikin kowace kasa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu