Gwamnatin jamhuriyar Benin ta samar da shirin bunkasa kiwo
Gwamnatin Jamhuriyar Benin tare da hadin gwiwar bankin raya kasashen Afirka ta samar da wani tsari na bunkasa sashen kiwo a arewaci da tsakiyar kasar.
Wallafawa ranar:
Kunna - 01:00
Matakin dake zuwa a wani lokaci da yan bindiga ke barrazana a wadanan wurare musaman arewacin kasar ta Benin.
A dan tsakanin nan Jamhuriyar Benin ta fuskanci hare-haren yan bindiga ,al'amarin dake kawo cikas ga ayukan makiyaya da manoma.
Shugaban kasar Patrice Talon ya nada Dokta Adamu Maman Sambo a mukamin babban jami'in hukumar kula da zamantakewar makiyayan kasar tare da gudunmuwar Bankin raya kasashen Afirka.
Dokta Adamu Maman Sambo babban jami’in hukumar kula da zamantakewar makiyaya a Jamhuriyar Benin ya bayyana mana irin ci gaba da wannan hukuma ta samu a dan tsakanin nan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu