Isa ga babban shafi

Sabuwar zanga-zangar kin jinin gwamnatin Sudan ta tsananta a rana ta 5

Jami’an tsaron Sudan sun yi amfani da hayaki mai sanya hawaye da kuma harsasan gaske don tarwatsa dandazon ‘yan kasar da suka tsunduma sabuwar zanga-zangar kin jinin gwamnatin mulkin Soji kwana na hudu a jere, wanda ke zuwa bayan kisan fararen hula 9 a alhamis din da ta gabata.

Masu zanga-zangar adawa da mulkin sojoji a Khartoum babban birnin kasar Sudan.
Masu zanga-zangar adawa da mulkin sojoji a Khartoum babban birnin kasar Sudan. AP - Marwan Ali
Talla

Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin da ke sanya idanu kan zanga-zangar ta Sudan sun ce jami’an tsaron na amfani da harsasan gaske kan fararen hular, inda alkaluman wadanda suka mutu tun bayan faro zanga-zangar a watan Oktoban bara ke kaiwa 114 ciki har da  mutane 9 da aka kashe a alhamis din da ta gabata wanda shi ya sake harzuka masu gangamin.

Masu sanya idanun na ganin a wannan karon zanga-zangar ta sauya salo da wadda aka saba gani inda galibi masu zanga-zangar da suka yi zaman dirshan rike da kwalaye dauke da rubutun kiyayya ga gwamnatin ta Soji ke bayyanawa manema labarai cewa ba za su daina gangamin ba har sai kasar ta koma karkashin mulkin farar hula makwamanciyar gwamnatin da aka kafa bayan hambarar da gwamnatin Omar al-Bashir.

Jiya lahadi aka cika rana ta 4 da faro sabuwar zanga-zangar inda jami’an tsaro suka rika feshin ruwan zabi kan masu zanga-zangar wadanda bayanai ke cewa suna ci gaba da karuwa tare da rufe manyan titunan kasar baya ga kona tayoyi akan hanyoyi.

Guda cikin masu zanga-zangar Muayyad Mohamed da ke jagorantar wani rukuni na masu zaman dirshan a tsakar birnin Khartoum ya ce zasuu ci gaba da gangamin ko da za su kare, yayinda wata matashiya Soha mai shekaru 25 ke cewa sam baza su mika wuya ba, har sai muradinsu ya tabbata.

Shima wani da ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa AFP cewa sun fito kan tituna ne don neman ‘yanci zaman lafiya da kuma adalci tare da tilastawa Sojoji komawa Barikoki inda aka sansu ba fadar gwamnati ba.

Zuwa yanzu dai Majalisar dinkin duniya kungiyar AU da kuma IGAD na shiga tsakani don warware matsalar bayan shirya wata tattaunawar sulhu da tsagin fararen hula ya kauracewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.