Isa ga babban shafi

Dubban 'yan kasar Ghana sun yi zanga-zanga kan tsadar rayuwa

Dubban ‘yan Ghana musamman matasa sun gudanar da zanga-zanga a babban birnin kasar Accra domin nuna bacin ransu kan matsin rayuwa sakamakon tabarbarewar attalin arziki, laifin da suka dora kan gazawar gwamnati.

Wasu daga cikin jagororin zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a kasar Ghana.
Wasu daga cikin jagororin zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a kasar Ghana. © RFI hausa / Abdullah Sham'un Bako
Talla

Bayanai sun ce sai da jami’an tsaro suka yi amfani da barkonon tsohuwa domin tarwatsa masu zanga-zangar gudun kada lamarin ya kazanta.

Wasu hotunan bidiyo dake yawo a kafofin sadarwar zamani sun nuna yadda wasu daga cikin masu zanga-zangar suka rika jifan jami’an tsaro da duwatsu, lamarin ya janyo farfasa motocin dake ajiye a gefen hanya, cikinsu har da na ‘yan sanda.

Tun da farko dai wata kungiyar matasa mai suna ‘Arise Ghana’ ce ta kira da a gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnatin kasar ta Ghana a ranakun Talata da Laraba, wato 28 da kuma 29 ga watan Yunin shekarar 2022 da muke.

Wasu majiyoyi sun bayyana cewar, wani karin batu da ya sanya zanga-zangar ta samu karbuwa ga akasarin ‘yan kasar Ghana shi ne yadda ake zargin manyan jami’an jam’iyya mai mulki da mamaye filayen gwamnati ta haramtacciyar hanya, kuma daya daga cikin yankunan da manyan kusoshin ke wawashe filayen shi ne gandun dajin Achimota, lamarin da ya dade yana ci wa mutane tuwo a kwarya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.