Isa ga babban shafi
GHANA-SIYASA

Yan adawa sun yi zanga zanga akan tsadar rayuwa

Yan adawa a kasar Ghana sun gudanar da zanga zangar lumana a titunan birnin Accra domin bayyana damuwar su akan yadda shugaban kasa Nana Akufo-Addo ke tinkarar matsalar tattalin arzikin kasa da kuma bukatar yin adalci dangane da kashe wasu masu zanga zanga guda 2.

Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo
Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo CRISTINA ALDEHUELA AFP
Talla

Dubban mutane suka shiga zanga zangar rike da rubuce rubucen dake nuna cewar, ’kowa na shan wahala, a gyara kasa’ da kuma ‘Yan Ghana na mutuwa, Akufo-Addo ka tashi daga bacci’.

Wani daga cikin masu zanga zangar Alisu Ibrahim yace rundunar Yan Sandan kasar na cike da azzalumai tare da kungiyoyin Yan sa kai, ganin yadda suke kashe mutanen su.

Zanga zangar itace irin ta ta farko da babbar Jam’iyyar adawa ta NDC ta shirya tun daga watan Maris lokacin da kotun koli tayi watsi da kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasar da akayi wanda ya tabbatar da nasarar shugaba Akufo-Addo.

Tsohon shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama
Tsohon shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama AP - Gabriela Barnuevo

Shugaba Addo na ci gaba da fuskantar matsin lamba daga masu adawa da shi saboda matsalolin tattalin arzikin kasa wanda annobar korona ta haifar.

Wasu masu zanga zanga guda 2 sun mutu a Yankin Ashanti a watan jiya lokacin da suke korafi kan mutuwar wani matashi mai fafutukar kare hakkin Bil Adama Ibrahim ‘kaaka’ Mohammed.

Gwamnatin Ghana ta gabatar da sabbin haraji akan jama’ar kasar da kuma kara farashin man fetur domin kara yawan kudaden da take samu sakamakon bashin dake kan ta da kuma raguwar kudaden shigar da take samu saboda annobar korona.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.