Ghana zata kafa Bankin raya kasar bayan samun tallafi daga wani Bankin Turai
Shugaban Kasar Ghana Nana Akufo-Addo ya bayyana cewar kasar sa ta karbi tallafin euro miliyan 170 daga Bankin Zuba Jarin Turai na EIB domin kafa sabon Bankin kasa da aka yiwa suna ‘Development Bank of Ghana’.
Wallafawa ranar:
Akufo-Addo ya bayyana sabon bankin a matsayin daya daga cikin harsasan bunkasa tattalin arzikin Ghana da suka yiwa lakabi da ‘Shirin Obaatampa’ sakamakon illar cutar korona a kasar.
Shugaban ya bayyana fatar ganin bankin ya taka rawar da ta dace wajen bunkasa harkokin Yan kasuwa da kuma taimakawa gwamnati aiwatar da manufofin ta na cigaba.
Ministan harkokin wajen Ghana Shirley Ayorkoor Botchwey ta sanya hannu a yarjejeniyar karbar kudin, yayin da Dr Werner Hoyer, shugaban Bankin EIB ya sanya hannu a madadin bankin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu