Isa ga babban shafi
Ghana

Ghana ta dakatar da aikin ceto a wata haramtacciyar mahaka da ta rufta

Hukumomin kasar Ghana sun dakatar da aikin ceto a wani wajen hakar ma’adinai sakamakon ruftawar da rami ya yi akan wasu masu aikin haka ba tare da izini ba, saboda hadarin da ke tattare da aikin.

Wata mahakar ma'adinai.
Wata mahakar ma'adinai. Glenn ARCOS AFP
Talla

Tuni aka zakulo gawarwakin mutane 3 daga cikin mahakar da ke ciki a yankin Breman, yayin da hukumomi suka kaddamar da bincike kan lamarin.

Gwamnatin Ghana ta haramta hakar ma’adinai a yankin, amma bayanan da ke zuwa na nuna cewar cikin dare wadannan mahaka suka je suna aiki kafin samun hadarin.

Tuni aka kama mutuum guda sakamakon hadarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.