Isa ga babban shafi
Ghana

'Yan sandan Ghana sun tsamo gawar matasa 12 da suka nutse a ruwa

Rundunar ‘yansandan kasar Ghana ta tabbatar da mutuwar wasu matasa 12 da wadanda suka karya dokokin yaki da coronavirus ta hanyar gudanar da taro a wuraren shakatawa na bakin ruwa, wanda ya kai ga nutsewarsu tare da rasa rayukansu.

Gawar wani da ya nutse a ruwar Mexico a ranar 24 ga watan Yunin 2019
Gawar wani da ya nutse a ruwar Mexico a ranar 24 ga watan Yunin 2019 REUTERS/Stringer
Talla

Rundunar ‘yansandan ta bakin kakakinta Irene Oppong a birnin Accra ta ce tawagar matasan wadanda shekarunsu ya fara daga 14 zuwa 17 sun gudanar da wani gangamin shagali a bakin ruwan Apam mai tazarar kilomita 80 da birnin Accra duk da haramcin da gwamnati ta yi na makamancin gangamin don yaki da Covid-19. 

Majiyar ‘yansandan wadda ta ce kawo yanzu ba a kai ga gano dalilin da ya kai ga nutsuwar matasan a ruwan ba, ta ce tun cikin watan Maris din bara kasar ta yi umarnin kulle dukkanin wuraren shakatawar bakin ruwa, don yaki da Covid-19.

A cewar Mr Oppong sun yi nasarar tsamo gawarwakin matasan 12 ciki har da mata 2, yayinda suka yi nasarar ceto rayukan wasu 2 bayan gaggauta kai su asibiti.

Majiyar ta ce har yanzu ta na ci gaba da laluben gangar jikin wadanda suka nutse a ruwan da kuma binciken musabbabin iftila'in.

Zuwa yanzu dai mutum dubu 86 da 465 Ghana ta samu masu coronavirus ciki har da mutum 647 da cutar ta kashe tun bayan barkewarta a bara zuwa yanzu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.