Isa ga babban shafi
Ghana

Ghana ta zama kasar farko da ta karbi alluran rigakafi karkashin shirin COVAX

Ghana ta zama kasar farko a Duniya da ta karbi alluran rigakafin coronavirus karkashin shirin Majalisar Dinkin Duniya na COVAX inda a yau juma’a alluran AstraZeneca dubu 600 suka isa birnin Accra daga India.

A ranar 2 ga watan Maris ne Ghana ke shirin fara yiwa jama'arta rigakafin na Coronavirus.
A ranar 2 ga watan Maris ne Ghana ke shirin fara yiwa jama'arta rigakafin na Coronavirus. REUTERS - Dado Ruvic
Talla

Tun da safiyar yau Laraba ne alluran suka isa babban filin jirgin saman Kotoka da ke Accra bisa rakiyar manyan jami’an hukumar UNICEF da ke matsayin karon farko da shirin na COVAX ya isar da alluransa wata karamar kasa a yammacin Nahiyar Afrika.

Ghana na cikin kasashen farko farko da suka sanya hannu a shirin na COVAX da ya kunshi kasashe 92 kamar yadda ministan labaran kasar Kojo Oppong Kkrumah ya shaidawa manema labarai.

Kasar ta yammacin Afrika mai yawan jama’a miliyan 30 alkaluman hukumar lafiyar kasar sun bayyana yadda ta samu jumullar mutum dubu 81 da 245 da suka kamu da cutar ciki har da wasu 584 da suka mutu.

Alluran dubu 600 kamar yadda Ghana ta sanar za a raba aikin rigakafin rukuni rukuni ta yadda gangaminsu zai fara ranar 2 ga watan Maris mai kamawa wanda zai shafi wadanda shekarunsu ya kai 60 zuwa sama sai kuma masu cutukan da ke cikin hadari, baya ga manyan jami’an gwamnati, ‘yan majalisu da alkalai da lauyoyi kana manyan ma’aikata.

Wata sanarwar hadakar UNICEF da WHO ta fitar ce ta tabbatar da isowar alluran Ghana a wani yunkuri na dakile yaduwar cutar wadda ke ci gaba da kisa.

Nahiyar Afrika da shirin COVAX

Galibin kasashen Afrika sun yi rijista da shirin na COVAX karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya wanda zai saukaka samar da  wadatattun alluran rigakafin Coronavirus ba tare da banbanta manyan kasashe akan kanana ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.