Isa ga babban shafi
GHANA-SIYASA

Jami'an tsaro sun kashe masu zanga-zanga a Ghana

Jami'an tsaro a kasar Ghana sun harbe wasu matasa guda 2 har lahira lokacin da suke gudanar da zanga zangar lumana domin bayyana bacin ran su da kashe wani jagoran matasa Ibrahim Kaaka Mohammed a Yankin Kudancin Ashanti.

Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo
Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo AFP - CRISTINA ALDEHUELA
Talla

Rahotanni sun ce jami’an Yan sanda da sojoji sun yi arangama da masu zanga zangar a garin Ejura abinda yayi sanadiyar rasa rayukan mutane 2 kamar yadda kakakin Yan Sanda Godwin Ahianyo ya tabbatar.

Jami’in yace suna gudanar da bincike akan lamarin kuma ya zuwa wannan lokaci hankali ya fara kwanciya a yankin bayan tashin hankalin da aka gani.

Wani jami’in kula da lafiya a yankin da ake kira Manyee Mensah dake aiki a asibitin gwamnati yace bayan mutane 2 da suka mutu wasu guda 4 kuma sun samu raunuka, kuma guda daga cikin su na cikin mawuyacin hali.

Wasu Yan bindigar da ba’a iya tantancewa ba ake zargi da hallaka Mohammed wanda yayi kaurin suna wajen sukar gwamnatin Ghana lokacin da suka kai masa hari  kusa da gidan sa dake Ejura.

Shugaban kasa Nana Akufo-Addo ya bukaci gabatar da rahotan bincike akan lamarin a cikin kwanaki 10 masu zuwa, bayan ya bayyana kaduwar sa da mutuwar mutanen guda 3.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.