Isa ga babban shafi
GHANA-KORONA

'Yan kasuwar Ghana sun gudanar da zanga zangar lumana

'Yan Kasuwa a kasar Ghana sun gudanar da zanga zangar lumana kusa da iyakar Cote d’Ivoire domin gabatar da bukatar su ga shugaban kasa Nana Akufo-Addo domin bude iyakokin kasar da aka rufe sakamakon dakile annobar korona.

Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo
Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo © RFI/France24
Talla

Zanga zangar da akayi a Elubo dake yammacin birnin Accra, itace ta biyu da aka gani a wannan mako bayan wadda akayi a Aflao dake kusa da iyakar Togo.

Ghana dake makotaka da kasashen Burkina Faso da Cote d’Ivoire da kuma Togo ta rufe iyakokin ta na sama da shekara guda domin dakile yaduwar cutar Covid-19, inda aka bar motocin daukar kaya kawai su dinga jigila.

Masu zanga zangar sanye da kayan dake nuna alamar tutar kasar a Elubo sun yi ta rera taken kasa suna kada ganga da kuma daga allunan dake dauke da rubuce rubucen dake bayyana irin halin kuncin da suka samu kan su.

Daya daga cikin kasuwannin Ghana
Daya daga cikin kasuwannin Ghana Getty Images - Merten Snijders

Masu zanga zangar sun roki shugaban kasa Akufo-Addo da yaji kukan da suke yi domin daukar matakin saukaka musu halin da suka samu kan su.

Dorcas Affo-Toffey, wata Yar majalisa daga jam’iyyar adawa tace suna bukatar shugaban ya dauki mataki cikin makwanni biyu masu zuwa, inda take tamabayar cewar menene dalilin bude tashar jiragen sama amma kuma iyakokin da ake shiga kasar ta mota suna rufe?

Ernest Kwoffi, wakilin karamar hukumar yankin yace an dauki matakin ci gaba da rufe iyakokin ne domin kare lafiyar jama’a daga cutar korona, amma yayi alkawarin mika kukan su ga shugabannin sa.

Fadar shugaban kasar tace tana tsara yadda za’a dinga gwajin masu tsallaka iyakokin kasar ne, kuma da zaran an gama za’a bude su.

Kasar Ghana na daya daga cikin kasashen da suka fuskanci koma bayan tattalin arziki sakamakon annobar korona wadda ta yiwa kasashe da dama illa.

Yan kasar sama da 119,000 suka harbu da cutar tun bayan barkewar ta, kuma sama da 1,000 daga cikin su sun mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.