Isa ga babban shafi

Boko Haram ta kashe fararen hula 4 da Sojoji 3 a Kamaru

Majiyoyin tsaro a kasar Kamaru sun ce mayakan boko haram sun hallaka fararen hula 4 da sojoji 3 a Jihar Arewa mai nisa da ke kasar.

Wasu Sojin Kamaru.
Wasu Sojin Kamaru. AP - Sunday Alamba
Talla

Wani jami’in hukumar yankin ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar mayakan boko haram ne suka kai hari a sansanin soji daHitawa akan iyakar Kamaru da Najeriya safiyar Talatar da ta gabata.

Jami’in ya tabbatar da cewar mutane 7 suka mutu sakamakon harin, wanda ya kunshi fararen hula guda 4 da sojoji guda 3.

Mayakan boko haram da ISWAP sun dade suna kai munanan hare hare a arewacin Kamaru da kuma kasashen Najeriya da Nijar da kuma Chadi.

Akalla mutane sama da dubu 36 suka mutu sakamakon rikicin boko haram wanda ya fara a shekarar 2009.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.