Isa ga babban shafi

'Yar gwagwarmayar kare hakkin mata a Sudan ta samu lambar yabo ta Duniya

Wata ‘yar gwagwarmayar Sudan Amira Osman Hamed ta samu lambar yabo a fafutukar da ta ke wajen tabbatar da kare hakkin dan adam, sakamakon gwagwarmayar fiye da shekaru 20 da ta shafe ta na yi kasar ta Arewacin Afrika, lambar yabon da kungiyar Front Line Defenders da ke Dublin ta yi bikin bayarwa a yau juma’a.

Wata zanga-zangar kin jinin gwamnati a Sudan.
Wata zanga-zangar kin jinin gwamnati a Sudan. © AP Photo/Marwan Ali
Talla

‘Yar gwagwarmayar kuma Injiniya Amira Osman Hameed da ta shafe shekaru fiye da 20 ta na kokarin tabbatar da kare dokokin hakkin dan adama a Sudan, ta shiga sahun masu irin wannan fafutuka daga kasashen Afghanistan da Belarus da Zimbabwe da kuma Mexico da suka samu lambar yabo daga hukumar kare hakkin dan adam ta Duniya.

Lambar yabon ta kungiyar Front Line Defenders, da aka fara bayarwa a 2005 akan girmama ‘yan gwagwarmayar tabbatar da kare hakkin dan dama da rayuwarsu ke cikin hadari a sassan Duniya, inda a wannan karon Amira Hemeed ta lashe kasancewarta wadda ta sha dauri a baya-bayan nan sakamakon jagorantar zanga-zangar adawa da mulkin Soji a Sudan.

A shekarar 2002 Amira ta fara shan dauri sakamakon kama ta da laifin saka wando yayinda a shekarar 2013 aka sake garkame ta da laifin kin sanya mayafi ko dan kwali don rufe kanta.

Baya ga gwagawarmayar tabbatar da kare hakkin dan adam Amira ta yi kaurin suna wajen sauya rayuwar miliyoyin mata a Sudan bayan da ta tsaya kai da fara wajen kare hakkin matan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.