Isa ga babban shafi

Babbar kungiyar kwadagon Tunisia ta yi watsi da tayin shiga tattaunawar kasa

Babbar kungiyar kwadagon Tunisia UGTT ta yi watsi da tayin shiga babban taron tattaunawar kasar da zai kai ga samar da gyara ga kundin tsarin mulkin kasar wanda shugaba Kais Saied ya kira, bayan da wasu bayanai ke cewa taron bazai gayyaci kungiyoyin fararen hula ba.

Al'ummar Tunisia na ci gaba da kalubalantar salon kamun ludayin shugaba Kais Sa'ied.
Al'ummar Tunisia na ci gaba da kalubalantar salon kamun ludayin shugaba Kais Sa'ied. AP - Hassene Dridi
Talla

Wasu bayanai sun ce gwamnatin shugaba Kais Saied ba ta gayyaci jiga-jigan wakilan al’umma daga sassan kasar da kuma kungiyoyin fararen hula don shiga taron ba, a kokarin samar da zaman lafiya a kasar da ke fama da rikicin siyasa tun bayan matakan shugaban na rushe gwamnati.

A watan Yulin bara ne shugaba Saied ya kori ilahirin mukarraban gwamnatinsa gabanin rushe majalisa tare da kwace ikon bangaren shari’a a wani yanayi da ‘yan adawa suka kira da juyin mulki ga tsarin demokradiyya, lamarin da ya jefa kasar a rikicin siyasa.

Shugaban na Tunisia ya cire jam’iyyun siyasa daga shiga duk wata tattaunawar samar da zaman lafiya da zai jagoranta, duk da kiraye-kirayen da ake masa daga kasashen ketare na ganin ya fadada yawan mahalarta taron don maslahar kasar.

A farkon watan da muek ciki na Mayu ne shugaba Kais ya amince da zaman tattaunawar ko da ya ke yaci gaba da caccakar bangarorin siyasa wadanda ya bayyana a matsayin koma baya ga Tunisia, yayinda a juma’ar da ta gabata shugaban ya sanar da sunan kungiyar ta UGTT a sahun wadanda za su shiga tattaunawar.

Sai dai sanarwar da kungiyar ta fitar jiya litinin, ta ce sam baza ta shiga duk wata tattaunawa da shugaba Kais Sa’id ya gayyata ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.