Isa ga babban shafi
zimbabwe

Zimbabwe: Matafiya taron Easter 35 sun mutu a hatsarin mota

Akalla mutane 35 ne suka mutu yayin da 71 suka jikkata a Zimbabwe, lokacin da wata motar bas dauke da mabiya addinin kirista zuwa wani taron Easter ta kauce hanya, ta fada wani kwazazzabo, kamar yadda ‘yan sanda suka baiyana a ranar Juma’a. Motar dai na dauke ne da mambobin wata majami’a ce ta Sihiyona bisa halartar taron Easter a kudancin kasar.

Wani mota da yayi mummunar hadari
Wani mota da yayi mummunar hadari © africafeeds
Talla

Ya zuwa yanzu dai adadin wadanda suka mutu ya kai 35, wadanda suka jikkata kuma 71, a cewar mataimakin kwamishinan 'yan sanda Paul Nyathi kamar yadda ya baiyana wa  Kamfanin Dillancin Labaran Faransa.

Alamu sun nuna cewa bas din ta yi lodi ne wanda ya zarce kima, kwamishinan ya  kara da cewa bas a Zimbabwe yawanci suna da takaitaccen nauyin fasinjoji daga 60 zuwa 75.

Ya cigaba da cewa maimakon a matsayin su na limaman coci su aikata abin koyi sai ya zamanto sun saba dokar data hana lodi da ya zarce kima domin bas a dokar Zimbwe bata lodin abin da ya zarce nauyin da aka kaiyade, abin da kullum doka ta hana.

Rundunar ‘Yan sandan tace bas din ta taso ne daga kudu maso gabashin garin Chimanimani zuwa Masvingo mai tazarar kilomita 280, kuma hatsarin ya afku ne a kusa da garin Chipinge.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.