Isa ga babban shafi

Libya ta samu Firaminista guda biyu

Kasar Libya ta samu Firaministoci guda biyu dake jagorancin gwamnatin kasar bayan da Majalisar dokokin ta amince da wasu ministoci domin adawa da jagorancin Firaministan rikon kwarya Abdulhamid Dbeibah wanda yaki yarda ya sauka daga mukamin sa domin tsayawa takarar zabe.

Taron sassanta yan siyasar Libya bisa jagorancin  kasar Turkiya
Taron sassanta yan siyasar Libya bisa jagorancin kasar Turkiya VIA REUTERS - Media Office of the Prime Minist
Talla

Yayin kada kuri’ar da ake ganin zata jefa kasar cikin wani sabon rikici, Yan Majalisun sun amince da tsohon ministan cikin gida Fathi Bashangha a matsayin Firaminista da kuri’u 92 daga cikin 101 dake Majalisar.

Wani dan kasar Libya dake zanga-zanga na ganin an gudanar da zabe a kasar
Wani dan kasar Libya dake zanga-zanga na ganin an gudanar da zabe a kasar REUTERS - ESAM OMRAN AL-FETORI

Shugaban majalisar dokokin Aguila Saleh ya bayyana Bashaga a matsayin Firaminista matakin da zai bashi damar kafa sabuwar gwamnati domin maye gurbin Dbeibah wanda yace ba zai sauka daga kujerar sa ba har sai an gudanar da zabe.

An dai nada Dbeibah Firaminista ne bara domin jagorancin gwamnatin rikon kwarya har zuwa lokacin da za’ayi zabe, inda aka gindaya sharadin cewar ba zai tsaya takara ba. Bayan hawa karagar mulki, Dbeibah ya bayyana aniyar sa ta takara kuma yanzu haka yana cikin masu neman kujerar shugabancin Libya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.