Isa ga babban shafi
Libya-'yan ci-rani

'Yan ci-rani 160 sun mutu a tekun Libya

A kalla 'yan ci rani 160 suka rasa rayukansu bayan da kwale-kwalensu ya nutse a gabar ruwan kasar Libiya a makon da ya gabata kamar yadda Hukumar  Kula da Tafiye-tafiye ta Duniya OIM ta sanar.

EUROPE-MIGRANTS/FRANCE-CALAIS
EUROPE-MIGRANTS/FRANCE-CALAIS © REUTERS - POOL
Talla

A cikin makon da ya gabata, akalla mutane 160 ne suka rasa rayukansu a yankin tsakkiyar tekun  Méditerranée, dab da gabar ruwan kasar Libya kamar yadda kakakin Hukumar Tafiye-tafiye ta Duniya da ke birnin Janiva, Safa Msehli ya sanar.

Bayan da kimanin bakin haure dubu dubu 1 da 500 suka nutse ta wannan hanya a shekarar bana.

Tsakanin ranakun 12 da 18 ga wannan watan nan na Disamba,  'yan ci-rani 466 ne aka ceto daga hallaka a gabar ruwan kasar ta Libya a cewar cibiyar OIM da ke kasar.

Kasashen yankin arewacin Afrika ne muhimmiyar hanyar da dubban matafiya ci rani ke bi a kowacce shekara da zumar isa gabar ruwan nahiyar  daga bangaren kasar Italiya a tafiyar kilomita 300 kacal ta tekun Méditerranée.

Mafi yawansu kuma, sun fito ne daga kasashen yankin saharar nahiyar Afrika, wadannan matafiya da ke neman mafaka galibinsu kuma na fadawa ne ga hannun masu safarar mutane idan ba su mutu ba a kokarinsu na tsallaka tekun.

Bayan da ta fada cikin mawuyacin rikicin siyasa tun bayan faduwar gwamnatin marigyayi Mouammar Kadhafi a 2011, kasar Libya ke ci gaba da  fuskantar suka kan yadda take tafiyar da rayuwar 'yan ci rani a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.