Hukumomin Ghana na tsare da Oliver Barker Vormawor
Hukumomin Ghana na tsare da wani dan gwagwarmaya da ake tuhumar da furta kalamai na yukunrin juyin mulki mudin gwamnatin kasar ba ta yi watsi da wani shirin ta na kawo gyara ga kudin tsarin mulki.
Wallafawa ranar:
Mutumen mai suna Oliver Barker Vormawor,shine shugaban gungun dake sa matsin lamba mai suna Fix The Country da ta sha shirya zanga-zanga a kasar ta Ghana don nuna adawar ta da manufofin gwamnatin wannan kasa.
Shugaban dake hannun hukuma na adawa ne da wani shirin hukumomin kasar na samar da sabuwar haraji da ta shafi sashen hada-hada ta kudade.
Kasar ta Ghana na fuskantar matsin lamba na tattalin arziki sanadiyyar basusuka da suka yiwa kasar yawa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu