Isa ga babban shafi
Ghana

Ghana ta ci tarar wani kamfani dala miliyan 6 saboda haddasa kisan mutane 13

Gwamnatin Ghana ta ci tarar wani kamfanin hakar ma’adinai tarar dala miliyan 6 saboda hadarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 13 a watan Janairu sakamakon fashewar motar dake dauke da nakiya.

Shugaban Ghana Nana Akufo Ado, yayin bukin ranar samun yancin kai a filin tunawa da yanci dake Accra, ranar 06 ga watan Maris shekarar 2021
Shugaban Ghana Nana Akufo Ado, yayin bukin ranar samun yancin kai a filin tunawa da yanci dake Accra, ranar 06 ga watan Maris shekarar 2021 © Ghana presidency
Talla

Fashewar nakiyar ta haifar da katon rami da kuma rushewar gidaje da dama kusa da birnin Bogoso dake da nisar kilomita 300 daga birnin Accra.

Hukumar agajin gaggawa a kasar tace bayan mutuwar mutane 13, hadarin ya raba mutane sama da 700 da muhallin su.

Ministan ma’adinai Samuel Jinapor ya sanar da cewar kamfanin Maxam Ghana dake sarrafa nakiyoyin ya sabawa dokokin hakar ma’adinai wajen safarar nakiyoyin.

Jinapor yace sakamakon nazarin da suka gudanar akan hadarin ya sanya tarar Dala miliyan guda akan kamfanin Maxam.

Ministan yace bayan tattaunawar da suka yi da shugabannin kamfanin, Maxam ya amince ya biya wasu karin Dala miliyan 5.

Tuni aka rufe kamfanin domin gudanar da bincike.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.