Guguwar Batsirai da ta ratsa Madagacar ta hallaka mutum 6
Akalla mutane shida ne suka mutu sakamakon guguwar da akayiwa lakabi da Batsirai mai karfin gaske da ta ratsa kasar Madagascar cikin daren Asabar zuwa Lahadi, lamarin da ya tilastawa mutane kusan 50,000 barin gidajensu tare da fuskantar hadarin ambaliya.
Wallafawa ranar:
Shugaban hukumar kula da bala'o'i a Madagascar, Paolo Emilio Raholinarivo, cikin wani sako da ya aikewa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya tabbatar da mutuwar mutane 6 sannan wasu kusan dubu 48 suka rasa matsugunansu, amatsayin bayanan wucin gadi.
Hukumomin Madagaska sun nuna cewa karfin guguwar ta ragu, saidai har yanzu akwai fargabar ambaliyar ruwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu