Isa ga babban shafi
Guinea - Juyin mulki

Ana Biciken Musabbabin Yunkurin Juyin Mulkin Guinea da Mutuwar Mutane 11

Sojan dake mulki a kasar Guinea-Bissau sun tabbatar da  shawo kan yunkurin juyin mulkin da aka samu Talata kuma rayukan mutane 11 suka salwanta sakamakon yunkurin.

Shugaba Umaro Sissoco Embalo yana bayani  dangane da tsallake rijiya da baya sakamakon yunkurin juyin mulki na ranar Talata.
Shugaba Umaro Sissoco Embalo yana bayani dangane da tsallake rijiya da baya sakamakon yunkurin juyin mulki na ranar Talata. Aliu EMBALO AFP
Talla

Bayanai na cewa an sami maido da zaman lafiya a birnin Guinea-Bissau kwana daya bayan da shugaba Umaro Sissoco Embalo ya tsallake rijiya da baya.

A ranar Talata data gabata wasu sojoji dauke da manyan bindigogi suka zagaye gidan gwamnati dake Bissau inda Shugaban kasar da kuma Firaminista ke taro.

Shugaba Embalo mai shekaru 49 ya shaidawa manema labarai cewa  ya yi katarin tsallake rijiya da baya, bayan kwashe sao’i biyar ana ta barin wuta da niyyar kwace  gwamnati.

Majiyoyin soja dake Guinea-Bissau sun shaidawa kamfanin Dillancin Labaran Faransa  AFP cewa sau hudu ana yunkurin juyin mulki  tun bayan samun ‘yanci daga Portugal a shekara ta 1974.

A yanzu haka hukumomin kasar sun kaddamar da cikakken binciken yumkurin juyin aikin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.