Isa ga babban shafi
Mali-Faransa-Diflomasiya

Gwamnatin sojin Mali ta sallami jakadan Faransa a kasar

Gwamnatin Kasar Mali ta bai wa Jakadan Faransa wa’adin sa’oi 72 da ya fice mata daga cikin kasa, abin da ke ci gaba da nuna tabarbarewar dangantakar kasashen biyu sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi.

Shugaban gwamnatin mulkin sojin Mali, Kanar Assimi Goita.
Shugaban gwamnatin mulkin sojin Mali, Kanar Assimi Goita. AP
Talla

Sanarwar gwamnatin sojin da aka karanta ta kafar talabijin ta ce tana sanar da jama’ar kasa da na kasashen duniya cewar ta bukaci Jakadan Faransa Joel Meyer da ya fice daga cikin yankin kasarta a cikin sa’oi 72.

Mali ta ce Faransa na ci gaba da yi mata zafafan kalaman tinzira da basu da tushe ballantana makama duk da korafin da take ci gaba da yi a kai.

Sanarwar ta ce gwamnatin Mali taki amincewa da kalaman da jami’an gwamnatin Faransa ke yi a kanta, wadanda suka saba wa yadda ake bunkasa hulda tsakanin kasashe biyu.

Mali ta ce a shirye take ta ci gaba da tuntuba da kuma daukar matakan da suka dace na hadin kai da kasashen duniya ciki har da Faransa wajen mutunta juna da kuma kauce wa yin katsalandan a harkokin cikin gidan kowacce kasa.

Dangantaka tsakanin Mali da Faransa ta yi tsami tun daga watan Agustan bara, lokacin da sojoji suka sake gudanar da juyin mulki na biyu a kasar.

A makon jiya Ministan harkokin wajen Faransa Jean Yves Le Drian ya bayyana gwamnatin sojin Mali a matsayin haramtacciya, kuma matakan da take dauka na rashin hankali ne, yayin da ministar tsaron kasar Florence Parly ta zargi shugabannin sojin da zafafa takalar Faransa.

Ministan harkokin wajen Mali, Abdoulaye Diop a ranar juma’a, ya zargi Faransa da nuna son kai wajen nuna kiyayyar ta da mulkin soji.

Diop ya zargi Faransa da zuwa wasu kasashe wajen dora shugabannin da suka yi juyin mulkin soji da kuma jinjina musu.

Kasar Faransa ta girke dubban dakarun ta a kasar Mali domin yaki da 'yan ta’adda a yankin Sahel.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.