Isa ga babban shafi
Mali- Faransa

Sojojin hayan Rasha na wawashe dukiyar Mali - Faransa

Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian ya zargi kamfanin samar da tsaro mai zaman kasansa Wagner na Rasha da wawashe dukiyar kasar Mali.

Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian yayin wani jawabi a kasar Jamus 10/09/2021.
Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian yayin wani jawabi a kasar Jamus 10/09/2021. AP - Jens Schlueter
Talla

Danganataka na kara tsami tsakanin mahukunatan Paris da gwamnatin mulkin sojan Mali a 'yan makonnin nan, ciki har da butun fitcewar dakarun kasashen Turai da aka tura yankin domin yakar masu da'awar jihadi.

A makon da ya gabata, Sojojin Amurka sun yi kiyasin cewa akwai daruruwan jami’an tsaron Wagner a yankin Sahel, amma rundunar sojin kasar ta ce hakan ba gaskiya ba ne.

Sojojin hayar Wagner "tsoffin sojojin Rasha ne, kuma kasar ta basu makamai kuma a kullum suna tare da rakiyar kayan aikin Rasha", in ji Le Drian.

" Yanzu haka suna amfani da albarkatun kasar Mali domin baiwa sojoji da sukayi juyin mulki kariya, suna lalata Mali," kamar yadda ya shaida wa jaridar Journal du Dimanche.

Majalisar Dinkin Duniya da Faransa da kuma kungiyoyin cikin gida sun ce kungiyar Wagner na aiki a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.