Ana zargin dakarun Mali da kisan wasu 'yan kasuwa na Mauritania
A wani kauye mai suna Nara daf da kan iyaka tsakanin Mali da kasar Mauritania, wasu yan kasuwa yan asalin Mauritania 7 ne suka rasa rayukan su inda ake zargin dakarun kasar Mali da hannu a wannan kisan wadanan yan kasuwa.
Wallafawa ranar:
Fadar shugaban kasar Mauritania a wata sanarwa mai dauke da sanya hannun shugaban kasar Mohamed Ould Cheikh Ghazouani ta bayyana bacin ran ta,inda shugaban kasar ta Mauritania ya aike da Ministocin harakokin wajen kasar,na tsaro,ministan cikin gida da shugaban hukumar lekken asirin Mauritania birnin Bamako ,za a gudanar da bincike tare da daukar matakan hukunta mutanen da suka aikata wannan kisa.
Gwamnatin sojin Mali ta shirya don bayar da hadin kanta na ganin an gudanar da bincike dangane da wannan kisa na yan kasuwar kasar Mauritania.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu