Isa ga babban shafi

Mutane 17 sun rasa rayukansu sakamakon fashewar bama-bamai a Ghana

Akalla mutane 17 ne suka mutu yayin da wasu 59 suka jikkata a ranar Alhamis, sakamakon fashewar bama-bamai ko kuma nakiyoyin da ake amfani dasu wajen fasa duwatsu da hakar ma’adanai a yammacin kasar Ghana bayan wata babbar mota dauke da nakiyoyin ta yi karo da wani babur.

Yankin Apiate na kasar Ghana,biyo bayan fashewar bama-bamai
Yankin Apiate na kasar Ghana,biyo bayan fashewar bama-bamai AFP - ERIC YAW ADJEI
Talla

Ministan yada labaran  kasar Kojo Oppond Nkrumah ya tabbatar da faruwar lamarin, yayin da mataimakin shugaban hukumar agajin gaggawa Sedzi Sadzi Amedonu ke cewa kusan gidaje 500 ne suka kone sakamakon wannan fashewar.

Fashewar ta bar wani katon rami tare da mayar da gine-gine da dama zuwa tulin baraguzan da itace da kuma karafa da kura suka lullube a yankin na Apiate da ke kusa da birnin Bogoso mai tazarar kilomita 300 daga babban birnin kasar Accra mai arzikin ma'adinai a kasar da ke yammacin Afirka.

Fashewar bama-bamai a yankin Apiate na kasar Ghana
Fashewar bama-bamai a yankin Apiate na kasar Ghana © Eric Yaw Adjei/ConnectFM/TV3 / AFP

Hotunan da Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya tabbatar, ya nuna yadda mutanen yankin ke garzayawa zuwa ga inda lamarin ya faru, inda hayaki ya turnuke saboda gobarar da ta tashi, yayin da masu aikin ceto suka dukufa wajen aikin bincika cikin baraguzan gine-ginen da suka rushe domin gano wadanda suka tsira da rayukansu.

Mutanen wannan yankin na cikin jimami da kaduwa,inda wasu rahotanni daga yankin ke tabbatar da cewa yan lokuta kafin aukuwar iftila'in,direban motar shake da bama-bamai da wani kamfanin hako ma'adinai na yankin ke amfani da su,ya kira jama'a da su kaucewa wannan wuri yan lokuta kafin fashewar wadanan bama-bamai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.