Isa ga babban shafi
GHANA-KORONA

Bankin Turai ya baiwa Ghana Euro miliyan 80 domin yaki da korona

Bankin Zuba jarin kasashen Turai ya bayyana shirin tallafawa gwamnatin kasar Ghana da kudin da ya zarce euro miliyan 80 domin inganta shirin yaki da annobar korona.

Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo da shugaban Bankin Zuba Jarin Turai  Werner Hoyer
Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo da shugaban Bankin Zuba Jarin Turai Werner Hoyer © Ghana Presidency
Talla

Fadar shugaban kasar Ghana tace za’a yi amfani da kudin ne wajen inganta cibiyoyin kula da lafiya da samar da kayayyakin kula da lafiyar da ake bukata a fadin kasar baki daya.

Shugaba Nana Akufo-Addo ya rattaba hannu akan yarjejeniyar karbar tallafin a wani bikin da akayi a Cibiyar bakin dake Luxembourg.

Mataimakin ministan harkokin wajen Ghana Kwaku Ampratwum Sarpong ya rattaba hannu akan yarjejeniyar a madadin kasar sa, yayin da Ambroise Fayolle, mataimakin shugaban bankin zuba jarin Turai ya sanya hannu a madadin bankin, kuma anyi bikin ne a gaban shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo da shugaban bankin Werner Hoyer.

Akufo-Addo ya bayyana cewar inganta dangantaka tsakanin bankin da kasashen Afirka na da matukar muhimmanci musamman wajen zuba jari a yankin Afirka dake kudu da sahara.

Shugaban Bankin zuba jarin Werner Hoyer ya yaba da matakin da Ghana ta dauka na rage radadin annobar korona ta hanyar zuba jari a bangaren kiwon lafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.