Isa ga babban shafi
Ghana

Anbaliyar Teku Ta Yiwa Mutane 4,000 Barna A Ghana

A kasar Ghana mutane akalla 4,000 suka rasa muhalli sakamakon igiyar ruwa daga teku da ta share gidaje akalla 500 dake gaban ruwa na gunduman Volta.

Gaban tekun kasar Ghana mai fuskantar ambaliyar ruwa.
Gaban tekun kasar Ghana mai fuskantar ambaliyar ruwa. NATALIJA GORMALOVA AFP
Talla

Kasashen yammacin Afrika da suka hada da Ghana na fama da ambaliyar ruwa daga teku dake barazana ga rayukan mutane.

A cewar kakakin Hukumar Agaji ta kasar Ghana George Ayisi tun ranar lahadi aka fara samun barazanar ambaliyar ruwa daga teku.

Ya bayyana cewa a yankin  Keta mutane 1,557 suka rasa matsuguni bayan da gidajensu  239 suka lalace.

A yankin gunduman Anloga kuwa mutane 1,394 suka shafu inda gidaje 134 suka lalace. Sai kuma yankin Arewacin Ketu inda mutane 1,027 suka shafu inda gidaje 149 suka lalace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.