Isa ga babban shafi
Ghana

Ghana ta fara sauraren ra'ayoyin jama'a kan luwadi

Majalisar Dokokin Ghana ta fara sauraron ra’ayoyin jama’a kan wani kudirin doka da zai kara dakile ‘yancin ‘yan luwadi, matakin da manyan kasashe da dama suka yi Allah wadai da shi.

Shugaban Ghana Nana Akufo-Ado.
Shugaban Ghana Nana Akufo-Ado. © Ghana presidency
Talla

Dabi’ar auren jinsi guda ko kuma luwadi,  laifi ne babba a Ghana, amma dokar da ake neman kafawa za ta kara tsananta hukunce-hukunce game da alakar ta dabi’ar auren jinsi guda,da kuma tsaurara hukunci kan duk wanda ke nema wa masu irin wannan dabi’a ‘yanci a kasar.

Ana sa ran Kwamitin da ke kula da Kundin Tsarin Mulki da Shari'a da na majalisar dokoki zai gudanar da taron na jin ra'ayin jama'a kan kudirin dokar tsawon makwanni 15 kafin a fara muhawara a majalisar.

Shugaban kasar ta Ghana Nana Akufo-Addo na cikin tsaka mai wuya dangane da amincewa ko kuma watsi da dokar, ganin cewa yana shan matsin lamba daga wasu kasashen duniya, amma kuma yana fuskantar turjiya a cikin gida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.