Fararen hula sun jikkata 'yan sanda 58 a zanga-zangar Sudan
Rundunar ‘yan sandan Sudan ta sanar da cewa jami’anta 58 suka jikkata yayin zanga-zangar jiya asabar a birnin Khartoum don kalubalantar mulkin soji a kasar.
Wallafawa ranar:
Yayin zanga-zangar ta jiya jami’an tsaro sun yi amfani da hayaki mai sanya hawaye don hana fararen hula afkawa motoci da gine-ginen jami’an tsaro don nuna fushinsu ga gwamnati.
Rundunar ‘yan sandan ta ce yayin zanga-zangar sun kame mutane 114 kuma za su gurfanar da su gaban kotu don amsa laifukan da suka aikata.
Majiyar ma’aikatar Lafiya a Sudan ta ce fararen hula 178 sun jikkata yayin zanga-zangar wadanda kuma galibi suka samu raunuka sanadiyyar duka ko kuma nuna musu karfi da jami’an tsraon kasar suka yi ciki har da mutum 8 da aka harba a makasa.
Haka zalika majiyar ta ce akwai kuma wasu mutum 48 da suka mutu a hannun jami’an tsaron yayin zanga-zangar galibinsu ta hanyar harbi ko kuma duka a makasa.
Wasu bayanai sun nuna cewa yayin zanga-zangar ta jiya Asabar, hukumomin Sudan sun katse layukan sadarwa ta yadda suka ci karensu babu babbaka kan fararen hula.
Zanga-zangar ta Sudan ta sake kazanta ne bayan mayar da Abdallah Hamdok kan karagar mulki a watan Nuwamba biyo bayan wata yarjejeniya da fararen hulan ke kallo a matsayin wadda bata karbu ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu