An tarwatsa masu zanga-zangar adawa da sojin Sudan
Dubban masu zanga-zanga sun yi tattaki a yau Asabar a Sudan, watanni biyu bayan sojojin kasar sun yi juyin mulki.
Wallafawa ranar:
Masu zanga-zangar na bukatar sojojin kasar da su gaggauta komawa barkokinsu, inda kuma suke son a mayar da cikakken karfin iko ga farar hula.
Masu zanga-zangar da ke rike da tutocin kasar, sun yi ta kada manyan gauguna tare da raye-raye da wake-wake a babban birnin Khartoum duk da cewa, an jibge jami’an tsaro masu tarin yawa.
Kodayake daga bisani rahotanni sun ce, jami’an tsaron sun yi amfani da hayaki mai sa-kwalla wajen tarwatsa dandazon masu zanga-zangar.
Akalla mutane 48 ne suka rasa rayukansu a tsawon makwannin da aka kwashe ana gudanar da zanga-zanga a Sudan kamar yadda wata kungiyar Likitocin Kasar ta bayyana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu