Isa ga babban shafi
Libya

Mayaka sun yi dandazo a Tripoli bayan sauke kwamandan askarawan kasar

Mayakan kungiyoyin da ke rike da makamai a Libya sun bazu a manyan titunan birnin Tripoli yau Alhamis a wani yunkuri na kalubalantar matakin tube babban kwamandan askarawan Sojin kasar daga mukaminsa da gwamnati ta yi.

Wani yanki na birnin Tripoli.
Wani yanki na birnin Tripoli. AFP - FATHI AL-MASRI
Talla

Wasu majiyoyin tsaro sun tabbatarwa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa tun da tsakar dare aka girke tarin bamanbantan mayaka daga kungiyoyin tsaro daban-daban da ke cikin kasar ta Libya dukkaninsu dauke da manyan makamai a wani yanayi da tuni al’ummar birnin suka shiga firgici da tsoron abin da ka iya biyo baya.

Matakin dai a cewar majiyar na zuwa ne sa’o’i kalilan bayan sauke Janar Abdulbasit Marwan daga matsayin babban kwamandan askarawan wanda aka maye gurbinsa da Janar Abdulkader Mansour, lamarin da ya tayar da hankalin magoya bayansa da kuma ake ganin su iya tayar da hatsaniya.

Janar Marwan wanda ya shafe tsawon shekaru yana jagorancin dakarun kasar mai fama da rikicin shekaru 10 yana samun cikakken goyon baya daga kungiyoyi masu rike da makamai a sassan Libya.

Wasu hotuna sun hasko yadda mayakan rike da muggan makamai da suka bayyana kansu a matsayin magoya bayan Marwan suka basu a tituna da kuma wasu manyan muhimman gine-gine ciki har da shalkwatar gwamnatin kasar inda ofishin firaministan rikon kwarya Abdulhamid Dbeiba ya ke.

Wannan mataki dai na zuwa ne kasa da mako biyu gabanin babban zaben kasar na ranar 24 ga watan nan a wani yunkuri na dawo da zaman lafiya kasar bayan yakin basasar shekaru 10.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.