Fada ya kaure tsakanin magoya bayan Khalifa Haftar da yan sandar Kasar
Fada da ya barke tsakanin magoya bayan janar Khalifa Haftar da yan Sanda cikin daren jiya litanin zuwa safiyar yau talata a birnin Tripolin na kasar Libiya.
Wallafawa ranar:
Wannan arrangama ta yi sanadiyar mutuwar mutane 2 wasu kuma da dama suka jikkata.
Wannan al’amari ya haifar da shakku ga yiyuwar gudanar da zabukan da kasar ke shirin yi a cikin wannan wata na Disemba.
Kasashen Duniya na ci gaba da kira ga bangarori da ke fada da junan su na ganin an cimma jituwa da za ta taimaka don dawo da zaman lafiya mai dorewa a kasar ta Libya.
Rikicin kasar Libya na tayar da hankulan kasashe dake raba iyaka da ita,musaman na yankin Sahel dake fatan ganin an kawo karshen wannan yaki ga baki daya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu