Isa ga babban shafi
fASHIN tEKU

Fashin teku na janyo asarar kudade ga Afirka - Majalisar Dinkin Duniya

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya ce yawaitar fashi a yankin tekun Guinea ta nahiyar Afirka ba barazana ce kawai ga jiragen ruwan Turai ba, tana ma janyo asarar dimbim kudade ga kasashen nahiyar.

Sojojin Najeriya na musamman dake yaki da fashin jiragen ruwa a tekun Guinea, shekarar 2019.
Sojojin Najeriya na musamman dake yaki da fashin jiragen ruwa a tekun Guinea, shekarar 2019. AFP
Talla

Rahoton, mai taken Pirates of the Gulf of Guinea, wato ‘Yan Fashin Yankin Tekun Guinea, ya ce an samu ayyukan fashi  har 106 a tekun a shekarar 2020, kana aka  yi garkuwa da masu aikin sufurin ruwa 623, a yankin wanda nan aka fi yin fashi a baya bayan nan.

Rahoton ya ce akasarin asarar kudaden da aka yi sakamakon  garkuwa da mutane, ta sauka ne a kan ‘yan kasashen waje, inda a shekarar da ta gabata, aka biya dala miliyan 5 a matsayin kudin fansa na ma’aikatan jiragen ruwa, wadanda ba ‘yan Afirka ba.

Sai dai ya ce kasashen da ke wannan yankin na Tekun Guinea ne za su fi jin radadin ayyukan masu fashin tekuda ke ci gaba da ta’azzara, duba da yadda ya zame musu dole su karfafa tsaro a  tekun.

Wannan rahoton na zuwa ne kusan makonni 2 bayan da wata tawagar sintiri ta sojin Denmark ta kashe ‘yan fashin teku 4 yayin wata musayar wuta a kusa da Najeriya.

Rahoton ya yi kiyasin cewa kudin da ake kashewa sakamakon ayyukan ‘yan fashin teku na iya kai wa dala biliyan 1 da miliyan dari 9 duk shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.