Isa ga babban shafi
TANZANIA

Ba zan bari a bata gwamnati na ba - Suluhu Hassan

Shugabar Kasar Tanzania Samia Suluhu Hassan ta zargi masu adawa da ita a cikin gwamnatin kasar da neman bata mata suna, abinda ke nuna barakar dake cikin jam’iyyar dake mulkin kasar.

Shugabar Tanzania Samia Suluhu Hassan
Shugabar Tanzania Samia Suluhu Hassan - AFP/File
Talla

Yayin da take tsokaci da murya mai karfi akan matsalar, Hassan tace wasu jami’an gwamnatin ta na neman bata mata suna tun bayan lokacin da ta zama shugabar kasar a watan Maris sakamakon mutuwar shugaba John Magufuli.

Shugabar tace wadannan mutane na zargin cewar cin hanci da rashawa ya koma cikin gwamnatin ta fiye da yadda aka saba gani kafin ta zama shugabar.

Shugabar gwamnatin Tanzania lokacin da ta kai ziyara Kenya
Shugabar gwamnatin Tanzania lokacin da ta kai ziyara Kenya © Ikulumawasliano

Hassan tace kowa ya san wannan matsalar ta samu ne a karkashin shugabannin da suka gabata, amma kuma wadannan mutane na neman dorawa gwamnatin ta alhaki, inda tace ba zata amince da haka ba.

Shugabar ta bayyana shirin rusa shugabannin gudanarwar tashoshin jiragen ruwan kasar da na hukumar dake kula da fito saboda amfani da kudaden gwamnati ta hanyar da bata kamata ba.

Shugaba Samia Suluhu Hassan lokacin da ta kai ziyarar aiki a Rwanda
Shugaba Samia Suluhu Hassan lokacin da ta kai ziyarar aiki a Rwanda © NewTimesRwanda

Rahotanni sun ce an samu baraka a Jam’iyyar Chama Cha Mapinduzi da take jagorancin Tanzania tun daga sjekarar 1961 tun bayan lokacin da Magufuli ya mutu, mataimakiyar sa Hassan ta karbi ragamar mulkin kasar.

A watan Agusta, an rufe Jaridar Jam’iyar mai mulkin Tanzania saboda wallafa labarin cewar Hassan ba zata tsaya takaran shugaban kasa a shekarar 2025 ba ba tare da gabatar da hujja ba.

Shugabar tace ana neman mata shaguben cewar ba zata tsaya takara ba ba tare da gabatar da wata hujjar da suka dogara da ita ba.

Samia Suluhu Hassan da tsohon shugaban kasa John Magufuli
Samia Suluhu Hassan da tsohon shugaban kasa John Magufuli AFP - ERICKY BONIPHACE

Hassan tace zasu sanya mace a gaba domin takarar zaben shekarar 2025 idan sun hada kan su a cikin jam’iyyar wajen yin aiki tare.

Rahotanni sun ce an samu baraka a cikin jam’iyyar dake mulkin kasar ne sakamakon kaucewa wasu manufofin tsohon shugaba John Magafuli da Hassan tayi, musamman abinda ya shafi nada mai sukar tsohon shugaban a matsayin minista da kuma kaddamar da rigakafin cutar korona wanda yaki amincewa da wanzuwar ta lokacin yana da rai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.