Tsohon Firaministan Lesotho ya gurfana gaban kotu kan zargin kisan Matarsa
Hukumomin Lesotho sun gurfanar da tsohon Firaministan kasar Thomas Thabane yau a kotun Maseru inda ake tuhumar sa da laifin kashe matar sa Lipolelo.
Wallafawa ranar:
Ana zargin Thabane mai shekaru 82 da daukar sojojin haya domin kashe Lipolelo a watan Yunin shekarar 2017, kwana biyu kafin rantsar da shi a matsayin Firaminista.
Akawun kotun Tebello Mokhoema ya karanta tuhume tuhumen da ake yiwa tsohon Firaministan da suka hada da daukar sojojin hayar domin hallaka Lipolelo Thabane a ranar 14 ga watan Yunin shekarar 2017.
Daga cikin mutane 5 da ake tuhuma da aikata kisan akwai amaryar sa Maesaiah wadda aka bada belin ta a watan Yuni, yayinda sauran 4 kuma 'yan bindigar da suka aikata kisan ne.
Rahotanni sun ce tsohon Firaministan da matar da aka kashe sun kwashe dogon lokaci suna rikici a tsakanin su, abinda ya kaiga neman bukatar saki a kotu.
‘Yan Sanda sun ce Thabane ya biya sojojin hayar dala dubu 24 domin kashe matar ta sa, kisan da ya yi sanadiyar raba shi da mukamin sa a watan Mayun shekarar 2020.
Tsohon Firaministan da amaryar sa sun ki amincewa da aikata laifin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu