Isa ga babban shafi
Habasha - Tigray

Fira Ministan Habasha ya sha alwashin yin murkushe ‘yan tawayen TPLF

Fira Ministan Habasha Abiy Ahmed ya sha alwashin yin murkushe ‘yan tawayen kasar cikin sakonsa na farko da ya aike daga fagen daga, a daidai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin rikicin da aka kwashe shekara guda ana yi, ya haifar da matsalar karancin abinci, mai munin gaske.

Fira Ministan Habasha Abiy Ahmed, yayin magana da manema labarai daga fagen dagar yaki da 'yan tawayen Tigray.
Fira Ministan Habasha Abiy Ahmed, yayin magana da manema labarai daga fagen dagar yaki da 'yan tawayen Tigray. © Twitter/Abiy Ahmed
Talla

Alwashin Abiy Ahmed na zuwa ne a yayin da ‘yan tawayen Tigray ke ikirarin samun galaba kan dakarun gwamnati, inda a baya bayanan suka sanar da kwace wani gari mai tazarar kilomita 220 daga Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha.

Tun a ranar Larabar da ta gabata, kafofin yada labaran Habasha suka rawaito cewa, Fira Minista Abiy, tsohon Laftanar-Kanar a soja, ya isa fagen daga domin jagorantar farmakin yaki da ‘yan tawayen yankin Tigray, inda ya mika ayyuka na yau da kullum ga mataimakinsa.

Yakin na Tigray dai ya janyo hasarar rayuka da dama, inda hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya WFP ta yi gargadin cewa adadin wadanda ke bukatar agajin abinci a arewacin kasar Habasha ya haura mutane miliyan tara, musamman a yankin Tigray da Amhara da kuma Afar.

Hukumar WFP ta ce al’amura sun tabarbare sosai a ‘yan watannin baya bayan nan, inda kimanin mutane miliyan 9 da dubu 400 ke fuskantar yunwa sakamakon yakin da ake gwabzawa tsakanin ‘yan tawayen TPLF da sojojin Habasha, idan aka kwatanta da kusan mutane miliyan bakwai dake cikin yunwar a watan Satumban da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.