Isa ga babban shafi
RFI-'Yan Jarida

RFI ta yi rashin daya daga cikin 'yan jaridarta

Daya daga cikin shahararrun masu gabatar da shirin tattalin arziki a Radio France International Stanislas Ndayishimiye ya rasu a birnin Paris bayan fama da rashin lafiya.

Stanislas Ndayishimiye
Stanislas Ndayishimiye © @ RFI Mandenkan
Talla

Stanislas Ndayishimiye dan asalin kasar Burundi ne da aka haifa a shekarar 1962, kuma ya share tsawon shekaru 28 yana zaune a Faransa.

Ndayishimiye, ya karanci ilimin taswirar duniya ne a jami’ar Bujumbura, kafin daga bisani ya fara aiki da radiyon gwamnatin kasar Burundi har ma ya rike mukamin babban edita.

Da farko dai ya je Faransa ne domin karanta aikin jarida a 1993, to sai dai watanni kadan bayan ya isa a kasar sai yakin basasa ya barke a Burundi, lamarin da ya sa ya nemi mafakar siyasa kuma ya samu a kasar ta Faransa.

Bayan fara aiki da sashen Afirka na Radio Farance International, marigayi Stanislas Ndayishimiye ya yi aiki a birnin Paris na tsawon shekaru, kafin ya wuce zuwa Abidjan kasar Cote d’ivoire jim kadan bayan faduwar gwamnatin Laurent Bagbo.

To sai dai kafin rasuwarsa, Ndayishimiye na aiki ne da sashen labaran tattalin arziki na RFI.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.