Isa ga babban shafi
Habasha - Tigray

Dakarun Habasha na gwabza yaki don kwace iko da garuruwa masu muhimmanci

Gwamnatin Habasha tace ana ci gaba da gwabza kazamin fada tsakanin dakarun ta da Yan Tawayen Tigray a wasu garuruwa guda 2 da suke iko da su a arewacin kasar.

Sojojin Habasha dake gwabza yaki da 'yan tawaye a yankin Tigray
Sojojin Habasha dake gwabza yaki da 'yan tawaye a yankin Tigray Amanuel Sileshi AFP/File
Talla

Mai Magana da yawun gwamnatin Legesse Tulu yace ana gwabza fadan ne a garuruwan Dessie da Kombolcha wadanda Yan Tawayen suka karbe iko da su a baya.

Kungiyar LTPF ta tabbatar da ci gaba da iko da garuruwan guda biyu, a daidai lokacin da bangarorin biyu ke fafatawa.

Mamayar na yankin Dessie, da yan tawayen Tigray suka yi a ranar Asabar, na nuni da irin nasarar da suka cimma, cikin irin hare haren da sukai ta yi na tsahon shekara guda, bayan karbe mafi akasarin yankin na Tigray daga dakarun kasar a watan Yuni tare da fadada wuraren da suka mallaka zuwa wasu sassa dake makobtaka da larduna na kasar

Amma ranar Lahadi, shaidun gani da ido sunce an samu barkewar luguden wuta a Birnin, yayin da dakarun kasar suka umarci fararen hula da su zauna cikin gidajen su, ba tare fita waje ba, duk da ja da baya da dakarun suka yi, a jaji beren wannan ranar

Har ila yau, mutanen garin sun ba da bayanin barke war ruwan wuta a garin Kombolcha dake kudancin Dessie, yayin da suka ce Yan tawayen na Tigray na kutsa wa kusa da babban Birnin Habasha wato Addi Ababa, a yayin da dakarun Gwamnatin Taraiyar kasar suka yi wa Yan Tawayen na Tigray barin wuta daga Sama

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.