Isa ga babban shafi
Canjin yanayi

Canjin yanayi na barazana ga 'yan Afirka fiye da miliyan 100 - MDD

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya nuna cewa, sama da mutane miliyan 100 ke fama da matsanancin talauci a Afirka inda ake fargabar akwai barazanar sauyin yanayi da ke tunkarar su, wanda kuma zai iya narkar da tsirarun dusar kankara da ke cikin nahiyar a cikin shekaru ashirin masu zuwa.

Yadda matsalar fari sakamakon Canjin Yanayi ta busar da madatsar ruwa a yankin Graaff-Reinet dake Afirka ta Kudu. Nuwamba 14, 2019.
Yadda matsalar fari sakamakon Canjin Yanayi ta busar da madatsar ruwa a yankin Graaff-Reinet dake Afirka ta Kudu. Nuwamba 14, 2019. © REUTERS/Mike Hutchings/File Photo
Talla

A cikin rahoton, Majalisar Dinkin Duniya ta yi karin haske kan kalubalen da ya addabi Afirka a shekarar bara, kama daga karancin abinci, talauci da kuma matsugunin jama'a.

Josefa Leonel Correia Sacko, kwamishinan lura da harkokin noma da raya karkara a Kungiyar kasashen Afirka ta AU, ya ce nan da zuwa shekarar 2030, an kiyasta cewa kusan mutane miliyan 118 za su fuskanci matsanancin talauci sakamakon fari, ambaliyar ruwa da matsanancin zafi a Afirka, idan ba a samar da matakan da suka dace ba.

A yankin kudu da hamadar sahara kuwa, sauyin yanayi na iya kara rage yawan kayayyakin da ake sarrafawa a cikin gida da kashi uku, zuwa shekarar 2050, in ji rahoton na Majalisar Dinkin Duniya.

Hukumar kula da yanayi ta duniya ta ce matsawar ana son gujewa aukuwar bala’o’i, akwai bukatar kasashen Afirka su samar da kayayyakin gwajin yanayi, ta yadda za a rika gargadin jama’a kafin lokaci ya kure don tunkarar hadurran da ke tafe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.